IQNA

An Gudanar Da Gasar Karatun Kur'ani Ta Mata A Kasar Turkiya

15:41 - July 15, 2009
Lambar Labari: 1802506
Bangaren kasa da kasa; An gudanar da gasar kur'ani mai tsarki ta mata a birnin Bali kasir na kasar Turkiya, inda gasar ta mayar da hanakali kan harda da kuma karatu gami da ilimin kyautata karatun kur'ani mai tsarki.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran habarceniz cewa; An gudanar da gasar kur'ani mai tsarki ta mata a birnin Bali kasir na kasar Turkiya, inda gasar ta mayar da hanakali kan harda da kuma karatu gami da ilimin kyautata karatun kur'ani mai tsarki. Bayanin ya ci gaba da cewa za a bayar da wani horo na musamman a cikin shirin, kuma dukkanin wadanda za su samu horon dai mata ne, kuma an kasa su zuwa kashi daban-daban, akwai wadanda suke cikin rukuni na 'yan shekaru 15, haka nan kuma akwai wadanda suke cikin rukuni na 'yan shekaru sama da haka har zuwa shekaru ashirin da biyar. Wanda ke jagorantar tawagar mahardata kur'ani ya ce hakan zai taimaka musu matuka wajen mayar da hankali kan hardar ta su.

433832
captcha