Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga jaridar shark al-ausat cewa; Qatar za ta dauki nauyin bakuncin taron kasa da kasa kan saka hannayen jari a mahangar addinin musulunci, wanda za a gudanar a cikin Agustan shekarar nan da muke ciki a birnin Doha fadar mulkin kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa wanan dai shi ne karo na hudu da za a gudanar da wannan taro, kuma zai mayar da hankali ne kan muhimman batutuwa da suka shafi harkokin kudi, da hakan ya hada da harkokin banki, saka hannayen jari a mahangar musulunci. Taron zai samu halarta masana daga kasashen daban-daban na musulmi da wasu kasashen da ba na musulmi ba, da nufin tattauna batutuwa na harkokin tattalin arziki a mahangar musulunci.
433877