Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki a jahar Calfornia ta kasar Amurka, a shirye-shiryen da musulmin jahar ke yin a fuskantar watan Ramadan mai alfarma, za a gudanar da gasar ne a babbar cibiyar musulmi ta jahar wato shura council.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet shura council cewa; Za a gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki a jahar Calfornia ta kasar Amurka, a shirye-shiryen da musulmin jahar ke yin a fuskantar watan Ramadan mai alfarma, za a gudanar da gasar ne a babbar cibiyar musulmi ta jahar wato shura council. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasar dai za ta hada matasa daga 'yan shekaru 6 har zuwa 'yan shekaru 18, wadanda za su gabatar da karatun kur'ani. Wasu daga cikinsu za su gabatar da karatun nasu ne a bangaren farko na kur'ani wasu kuma daga kasa zuwa rabin kur'ani wasu kuma za su gabatar da karatun ne daga sama zuwa kasa.
433852