Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Fransa cewa; An gabatar da shawarar kafa dokar hana mata musulmi malaman makaranta saka hijabin musulunci a makarantun da ke jahar Oregon ta kasar Amurka, wanda ake jiran 'yan majalisar jahar su amince da wannan ayar doka kafin fara aiki da ita. Bayanin ya ci gaba da cewa wasu daga cikin masu tsattsauran ra'ayin kiyayya daga cikin 'yan siyasar jahar ta Oregon ne suka gabatar da wannan daftarin kudiri ga majalisar, wanda kuma yanzu haka batun na hannun shugaban majalisar jahar, inda suke neman da bayar da dama ga dukkanin 'yan majalisa da su kada kuri'a kan amincewa ko rashin amincewa da wannan daftarin kudiri, wanda kuma da zaran sun amince da wannan ayar doka ba tare da bata lokaci ba za ta fara aiki a fadin jahar.
435199