Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; Alkalin alkalan kasar Iran Ayatollah Hashemi Shahrudi ya bayyana cewa; ya kamata kasashen musulmi musamman ma kasashen yankin gabas ta tsakiya da su yi amfani da abubuwan da suka hada su ta fuskacin shari'a, domin yin aiki kafada da kafada ta wannan bangaren ta yadda za a samu cikakkaiyar fahimtar juna da tamakekeniya a tsakaninsu.Ayatollah Hashemi Shahrudi ya bayyana hakan ne a jiya a lokacin da yake ganawa da jakadan kasar Oman a Iran, bayan da suka kammala salla a hubbaren Imam Khomeini da ke birnin Tehran.
436276