IQNA

An Gudanar Da Wani Shiri Na Horar Da Malaman Kur'ani A Afganistan

16:38 - July 21, 2009
Lambar Labari: 1804349
Bangaren kasa da kasa; An aiwatar da wani shiri na horar malaman makarantun kur'ani mai tsarki na kasar Afganistan, a babbar cibiyar kula da harkokin ilimi da bayar da horo ga malaman kur'ani.
Kamfanin dillancin labaran Ikna reshen kasar Afganistan ya habarta cewa; An aiwatar da wani shiri na horar malaman makarantun kur'ani mai tsarki na kasar Afganistan, a babbar cibiyar kula da harkokin ilimi da bayar da horo ga malaman kur'ani. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shiri ya kunshi abubuwa da dama, da hakan ya hada da koyar da malaman yadda za su koyar da yara hardar kur'ani mai tsarki bias hanya mafi sauki, da kuma hanyoyin karatu masu sauki ta yadda cikin kankanin lokaci za su iya koyar da mutane da dama su iya karatun kur'ani mai tsarki. Wannan dai shi ne karo na farko da aka fara gudanar da irin wannan shiri da kuma wannan salo a kasar Afganistan. Tuni al'ummomin kasar suka nuna gamsuwarsu dangane da sabbin hanyoyin koyarwa da aka bullo da su a makarantun kur'ani.

436075




captcha