IQNA

Bangaren al'adu da fasaha; An bude baje kolin gwagwarmayar musulunci a kasar Labanan a garin balabak da ke kudancin kasar Labanan, wanda kungiyar gwagwarmayar musulunci ta kasar labanan Hizbullah ta shirya gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga reshensa na birnin Beirut cewa; An bude baje kolin gwagwarmayar musulunci a kasar Labanan a garin balabak da ke kudancin kasar Labanan, wanda kungiyar gwagwarmayar musulunci ta kasar labanan Hizbullah ta shirya gudanarwa. Bayanin ya ci gaba da cewa an bude wannan baje kolin ne domin nuna wasu daga cikin hotuna da kayyakin yaki da aka yi amfani da su a lokacin yakin da Isra'ila ta kaddamar kan al'ummar kasar Labanan, inda ta kasha fararen hula sama da dubu daya da wasu daruruwa, tare da rushe gidajen fararen hula da cibiyoyin ilmi, da kuma masallatai gami da majami'oi. Baje kolin ya zo ne daidai lokacin da ake gudanar da bukuwan tanawa da sakin fursunonin yaki daga kurkukun Isra'ila.
436087