IQNA

Allah Masani Ne A Kan Komai

Allah bãbu abin bautãwa fãce Shi, Rãyayye, Majiɓincin halitta. Barci ba ya riske Shi. Shi ne da mulkin abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa. Wane ne wanda ke yin cẽto a wurinSa, fãce da izninSa? Yanã sanin abin da yake a gaba gare su da abin da ke bãyansu, kuma bã su kẽwayẽwa da kõme daga ilminSa, fãce da abin da Yake so. Al'arshinSa ya shimfiɗa bisa sammai da ƙasa, kuma tsarewarsu bã ya gajiyar da Shi. Kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma.