IQNA

Za A Raba Wasu Makaloli Na Yada Addinin Musulunci A Australia

10:34 - July 23, 2009
Lambar Labari: 1804600
Bangaren kasa da kasa; Gwamnatin kasar Australia ta kudiri aniyar buga wasu makaloli dangane da addinin muslunci domin raba su ga jami'n gwamnati, da nufin ba su damar samun masaniya kan addinin muslunci da koyarwarsa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet Dunya Bulteni cewa; Gwamnatin kasar Australia ta kudiri aniyar buga wasu makaloli dangane da addinin muslunci domin raba su ga jami'n gwamnati, da nufin ba su damar samun masaniya kan addinin muslunci da koyarwarsa. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shiri da gwamnatin Austaralia take da shi zai taimaka matuka wajen wayar da kan da dama daga cikin jami'anta wadanda suke da karancin masaniya dangane da addinin musulunci, wanda rashin samun masaniya dangane da addinin musulunci ne ya sanya wasu daga cikinsu suke yin matukar kiyayya da addinin muslunci.
436794



captcha