IQNA

La'akari Da Ma'anonin Kur'ani Ya Fi Muhimmanci A Kan Harda Da Karatu

17:38 - July 26, 2009
Lambar Labari: 1805949
Bangaren kasa da kasa; Daya daga cikin abin da ya ke da muhimmanci ga masu karatu da hardar kur'ani shi ne yin la'akari da manonin ayoyin da suke karantawa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren yada labarai na birnin Tehran cewa; daya daga cikin wadanda suka halarci gasar karatun kur'ani daga kasar Iraki Ali abdussalam ya bayyana cewa a cikin wata zantawa da ta hada shi da kamfanin dillancin labaran Ikna; Daya daga cikin abin da ya ke da muhimmanci ga masu karatu da hardar kur'ani shi ne yin la'akari da manonin ayoyin da suke karantawa, maimakon dogara kawai da zagwaron hardar ko kyautata sautin karatu ba tare da la'akari da manonin ayoyin ba.

438013

captcha