IQNA

Gasar Kur'ani Ta Kasa Da Kasa Tana Kara Fito Da Mahangar Kur'ani

17:37 - July 26, 2009
Lambar Labari: 1805951
Bangaren kasa da kasa; Gudanar da gasar kur'ani ta kasa da kasa na kara fito da mahangar kur'ani mai tsarki kan lamurra da dama da suka shafi rayuwar dan adam da ilimi da ke cikin kur'ani mai tsarki ga sauran al'ummomi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; a cikin wata zantawa da ta hada daya daga cikin makaranta da suka halarci gasar daga kasar Indonesia Mumahhad abdulshakur, ya bayyana cewa Gudanar da gasar kur'ani ta kasa da kasa na kara fito da mahangar kur'ani mai tsarki kan lamurra da dama da suka shafi rayuwar dan adam da ilimi da ke cikin kur'ani mai tsarki ga sauran al'ummomi. Ya ci gaba da cewa Daya daga cikin abin da ya ke da muhimmanci ga masu karatu da hardar kur'ani shi ne yin la'akari da manonin ayoyin da suke karantawa, maimakon dogara kawai da zagwaron hardar ko kyautata sautin karatu ba tare da la'akari da manonin ayoyin ba.

438011
captcha