IQNA

Makarantan Kur'ani Na Iran Sun Taka Rawar Gani A Wajen Gasa Ta Kasa Da kasa

13:45 - July 28, 2009
Lambar Labari: 1806347
Bangaren kasa da kasa; Iraniyawa sun taka rawar gani a wajen gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki da aka gudanar a birnin Tehran, inda suka samu yabo daga alkalan da suka yi alkalanci a cikin gasar daga kasashen duniya daban-daban.
Wani makarancin kur'ani daga kasar Syria da ya halarci gasar kur'ani ta duniya da aka gudanar a birnin Tehran ya bayyana cewa; Iraniyawa sun taka rawar gani a wajen gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki da aka gudanar a birnin Tehran, inda suka samu yabo daga alkalan da suka yi alkalanci a cikin gasar daga kasashen duniya daban-daban. Ammar Muhammad ya bayyana hakan e a cikin wata zantawa da ta hada shi da kamfanin dillancin labaran Ikna. Ya ci gaba da cewa Iraniyawa da suka halarci gasar sun yi amfani da salo na musamman karatu wanda ya burge kowa.

438169




captcha