Kamfanin dillancin labaran Ikna habarta cewa; Wani bincike ya tabbatar da cewa yanzu wasu daga cikin kasashen yammacin turai suna nan kan bakansu na kyamara ddinin muslunci da mabiya addinin a cikin kasashensu. Bayanin ya ci gaba da cewa idan aka kwatanta da lokutan baya inda da dama daga cikin al'ummomin nahiyar turai suka dauki tsananin gaba da addinin muslunci sakamakon siyasar da wasu kasashe suka dauka ta bayyana addinin musulunci a matsayin addinin tashin hankali, yanzu hakan ya ragu matuka a kasashe da daman a nahiyar.
440618