Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga bangaren yada labarai na hubbaren imam cewa; An gudanar da tarukan tunawa da zagayowar ranar haihuwar Imamul hujjah AJ a hubbaren Imam Khomeni da ke birnin Tehran a jiya. An buga tare da littafin matsayin addinin musulunci dangane da ilimi da kuma sanin kur'ani mai tsrki tare da koyon ilmominsa da yake dauke da su da ke shiryar dad an adam zuwa ga sahihin tafarki. Bayanin ya ci gaba da cewa wanna shafin internet zai mayar da hankali wajen yada al'amurra da suka shafi addinin musulunci, tare da mayar da martani kan shubhohin da ake yi kana addinin musulunci, domin kuwa daga cikin dalilan bude wannan shafi har da isar da sakon addinin musulunci ga wadan dab a musulmi ba, domin sanin irin koyarawar addini da kuma bayyana musu hakikanin abin da ke tattare da wannan addinin sabanin abin da makiya musulunci suke nunawa a shafukan internet.
444380