Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga wani malami mai suna Nasir Shukrian cewa; Sanin Imam zaman shi ne babban sirriin magance dukkanin matsalolin zamantakewa da kuma matsalolin matasa a cikin al'umma. Bayanin ya ci gaba da cewa Kwamitin wanda ya hada kungiyoyi da cibiyoyin addinin musulmunci sama da 40 daga sassa daban-daban na kasashen duniya, zai yi dubi ne a zaman nasa na birnin Tripoli kan muhimman batutuwa da suke ci ma al'ummar musulmi tuwo a kwarya a cikin wannan zamani, da hakan ya hada da cin zarafin da ake yi wa musulmi da mabiya addinin musulunci a wasu kasashe na yammacin turai, tare da daukar matakan da suka dace da nufin kawo karshen hakan.
444382