Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren yada labarai da hulda da jama'a na ma'aikatar kula da al'adu ta jamhuriyar Musulunci ta Iran cewa; Cibiyar kula da harkokin al'adu ta shirya gudanar da wasu taruka da ake yi wa taken makon kur'ani mai tsarki, wanda kuma za a gudanar da tarukan ne a kasashen duniya daban-daban, musamman ma dai kasashen musulmi. Bayanin ya ci gaba da cewa manufar gudanar da tarukan ita ce kara wayar da kan musulmi dangane da muhimamncin da ke tattare da raya harkokin karatun kur'ani a ko'ina cikin kasashen musulmi.
443996