Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na cibiyar kula da harkokin addini ta kasar hadaddiyar daular larabawa cewa; Za a gudanar da wani shiri na karatun kur'ani mai tsarki a kasar hadaddiyar daular larabawa a birnin Dubai bababn birnin kasuwancin kasar, wanda kuma wannan shi ne karo na uku da za a gudanar da irin wannan taro na karatun kur'ani a cikin watan Ramadan, wanda mahukuntan kasar suka shirya gudanarwa.
444704