Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto shugaban bangaren hulda da jama na cibiya gudanar da bincike da nazari kan rayuwar Imam Musa Sadr sayyid jawad cewa; Imam Musa Sadr ya taka gagarumar wajen magance da dama daga cikin matsalolin da aka yi ta samu tsakanin musulmi da kuma mabiya addinin kirista a kasar Labanan. Tasirin kokarin da Imam Musa Sadr ya yi wajen hada kan mabiya addinai a kasar labanan da kuma hada kan musulmi sunna da shi'a har yanzu ana cikin cin moriyarsa a kasar, da sauran kasashen yankin gabas ta tsakiya baki daya.
445218