IQNA

Za a Kafa Wata Makarantar Koyar Da Addinai A Kasar Jamus

16:58 - September 12, 2009
Lambar Labari: 1825192
Bangaren kasa da kasa; Za a bude wata makarantar firamare domin koyar da kananan yara addinai da aka safkar daga sama, wato addinan kiristanci da yahudanci da kuma kiristanci a birnin Osnaburg na kasar Jamus.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga majiyoyin majami'ar igmg ta birnin Osnabruck cewa; Za a bude wata makarantar firamare domin koyar da kananan yara addinai da aka safkar daga sama, wato addinan kiristanci da yahudanci da kuma kiristanci a birnin Osnaburg na kasar Jamus. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan na daya daga cikin kokarin da cibiyar kula da harkokin addinai mai zaman kanta ta kasar Jamus, domin samar da kyakkyawar fahimtar juna tsakanin dikkanin mabiya addinai da ka asafkar daga sama. Wannan shiri ya samu karbuwa daga miliyoyin mutanen kasar Jamus wadanda akasarnsu mabiya addinai kirista ne.

463588

captcha