IQNA

'Yan Shi'ar Pakistan Sun Gudanar Da Taron Manmema Labarai Kan Manufofin Shi'a

16:57 - September 12, 2009
Lambar Labari: 1825195
Bangaren kasa da kasa; An gudanar da wani zama tare damanema labarai na kasar Pakistan wanda mabiya mazhabar shi'a a kasar suka shirya gudanarwa, domin bayyana manufofinsu da kuma koyarwar akidarsu.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga kwamitin mabiya mazhabar shi'a cewa; An gudanar da wani zama tare damanema labarai na kasar Pakistan wanda mabiya mazhabar shi'a a kasar suka shirya gudanarwa, domin bayyana manufofinsu da kuma koyarwar akidarsu. Bayanin ya ci gaba da cewa babbar manufar gudanar da wannan taron ita ce kara wayar da kan al'umma musamman ma mabiya mazhabbin sunna wadanda su ne suka fi yawa akasar da su fahimci hakikanin manufofin mabiya mazhabar shi'a domin samun fahimta juna da zaman lafiya tsakanin dukkanin musulmi.
463026

captcha