IQNA

A Yau Ranar Kudus Ta Duniya Ta Samu Matsayi Da Haskakawa A Duniya

16:37 - September 13, 2009
Lambar Labari: 1825656
Bangaren siyasa : Mataimakin shugaban komitin shawara a Tehran ya yi imanin cewa: a yau bayan shekaru talatin da sanya sunan juma'a karshe ta watan Azumi a matsayin ranar Kudus ta duniya ta samu matsayi da karbuwa a duniya.
Hasan Biyadi mataimakin komitin shawara a Tehran a wata tattaunawa da cibiyar da ke kula da harkokin Kur'ani a Iran Ikna ya yi nuni da yadda ranar Kudus ta duniya ta samu karbuwa a tsakanin musulmai da duk wani mai son ganin an kare hakkin dan adam a duniya kamar yadda jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran a lokacin da yake gabatar da hudubar sallar juma'a ya bayyana .

463287

captcha