IQNA

Sheikh Qassem: Harin Pager jarabawa ce wadda ta kara wa masu gwagwarmaya kwarin gwiwa

13:48 - September 18, 2025
Lambar Labari: 3493889
IQNA - Babban sakataren kungiyar Hizbullah, Sheikh Naeem Qassem, ya yi jawabi ga wadanda suka tsira daga kisan Pager a bikin cika shekara guda.

Babban sakataren kungiyar Hizbullah, Sheikh Naim Qassem, ya yi jawabi ga wadanda suka tsira daga kisan Pager a bikin cika shekara guda da aiwatar da wannan harin ta’addanci da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta yi a ranar 17 ga Satumba, 2024.

“Ku ne masu gani na gaskiya, tushen begenmu, kuma sadaukarwar ku ga Allah ita ce ke ba wa rayuwa ma’anarta ta har abada, ku ne hasken da ke shiryar da mu domin bin hanya, kuma juriyarku ita ce zuciyar juriyarmu,” in ji Sheikh Qassem a cikin sakonsa ga mutanen da suka jikkata a harin.

“Me zan iya ce muku? Don yanzu ku ne malamai, masu ba da shawara, ku ne jagorori, saboda kun yi sadaukarwa kuma kuna a kan yi, ” in ji shi.

Babban magatakardar na Hizbullah ya yi nuni da dabi’u guda uku da ya  yi misali da wadanda harin ya rutsa da su da kuma rayuwarsu, na farko shi ne murmurewa, yayin da suke samun waraka daga raunukan da suka samu, kuma mafi mahimmanci, suna nan daram a kan bakansu. Ya bayyana hakan a matsayin jarabawa ce ta Ubangiji, wadda wadanda abin ya shafa suka samu nasarar cin wannan jarabawa.

 

 

 

4305619

 

captcha