Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Jordan cewa; Ana ci gaba da ajiye wani kwafin kur'ani mai tsarki da ya fi jimawa a dakin ajiye kayan tarihi na birnin Qods. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan kur'ani wanda tarihinsa ke komawa zuwa ga shekaru sama da dbu daya da dari biyu da suka gabata, ana bayyana shi a matsayin dadadden kur'ani, kuma yanzu haka masu kula da kayayyakin tarihi da ke gudanar da ayyukan abirnin Qods sun bayyana cewa kur'anin yana nan lafiya lau, ba tare da wani abu ya shafi takrdu ko rubutunsa ba. 463915