IQNA

An Gudanar Da Taron Buda Baki A birnin Moscow Na Kasar Rasha

11:27 - September 20, 2009
Lambar Labari: 1828051
Bangaren kasa da kasa; An gudanar da wani babban taron buda baki a birnin Moscow da ya hada manyan jami'an gwamnati da kuma malaman addinin musulunci da ma mabiya sauran addinai.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na islam online cewa; An gudanar da wani babban taron buda baki a birnin Moscow da ya hada manyan jami'an gwamnati da kuma malaman addinin musulunci da ma mabiya sauran addinai. Taron buda bakin wanda cibiyar kula da harkokin addinin musulunci ta birnin Moscow ta dauki nauyin shiryawa ya samu halartar mutane sama da 400, da suka hada jami'an gwamnati da malaman mazhabobin addnin musulunci gami da malamai daga sauran addinai. 467038
captcha