IQNA

Bangaren fikira; An yi bayani dangane da binciken da Aytaollah Reishahri ya gudanar a kan wasu bangarori hudu, wato karafa zamantakewar iyali, da kuma rike bakin aljihu, da hikimomin ma'aiki (SAW) da hikimomin Imam Ali (AS) duk a mahangar kur'ani da hadisi.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa; Aytaollah Mohammdi Reishahri daya ne daga cikin fitattun malami a Iran, wanda ya shahara da rubuce-rubuce a bangarori daban-daban na ilimi. An yi bayani dangane da binciken da Aytaollah Reishahri ya gudanar a kan wasu bangarori hudu, wato karafa zamantakewar iyali, da kuma rike bakin aljihu, da hikimomin ma'aiki (SAW) da hikimomin Imam Ali (AS) duk a mahangar kur'ani da hadisi. Wannan bayani bai takaitu da ambatar muhimman abubuwan da ya kawo na dalilai da ayoyin kur'ani ko hadisan ma'iki da na Imam Ali (AS) ba, a'a ya shiga cikin bayani na hankali domin tabbatar da hujja ta hankali da kowane mutum zai iya riskar bayaninsa, tare da amincewa da dukkanin dalilan da ya dogara da su. Ayatollah Reishahri ya rubuta wani littafi dangane da rayuwar iyali, wanda a cikin wannan littafi nasa ya kawo mahangar kur'ani dangae da rayuwar iyali da yadda ya kamata a gudanar da ita, bayan nan kuma sai ya kawo bayanai da suka da suka dangaci hadisai masu bayani kan rayuwar iyali, daga cikin hadisan akwai wadanda aka samo daga ma'aiki (SAW) da kuma hadisai da aka karbo daga limaman ahlul bait (AS) Bayan day a gama shimfidar bayaninsa da ayoyin kur'ani da hadisai, sai kuma ya shiga kawo batutuwa na manyan malamai wadanda suka rubuta dimbin littafai na hakan, da ma masana na zamani. Day a gama sai ya shiga nasa bayanin na ilimi da kuma na hankali. A cikin littafin ya yi kokarin rarrabe irin tasirin da zamantakewar iyali take haifarwa na gari ko kuma akasin haka. Ta yadda tarbiyar iyaye ta kan taka gagarumar wajen dora yaro kan kowace irin turba, turba ta tarbiya sahihiya ko akasin hakan. A bangarn guda kuma an yi bahasi a cikin littafinsa kan mahangar kur'ani da ma sunna dangane da yadda ya kamata mutum ya kula da tattalin arzikinsa, tare da kaucewa almubazzaranci wajen sarrafa dukiya a cikin rayuwa ta yau da kullum, da kuma bayanai na hankali da kowane mai karatu ko mai sauraro zai iya amince da su cikin sauki. Bayan kuma an bahasi a cikin littafinsa kan hikimomin manzon Allah (SAW) da kuma bahasi kan littafinsa na hiimomin Imam Ali(AS) tare da dogaro da hadisai da sanadinsu. Bayanin da mayar da hankali kansa danganeda hikimar Imam Ali (AS) ya dogara ne kaco kaf a kan hadisan da ka harhada na Imam Ali (AS) a cikin littafin Nahjul balaga, wanda ya shahara a duniya ta fuskacin bayanin hikimomin Imam Ali (AS) da kuma ake komawa zuwa gare shi wajen dogara da hadisan ko kalamansa. 468323