Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na Nasij cewa; Za a gudanar da wani zaman taro domin gudanar da tattaunawa tsakanin mabiya addinai a birnin Jenneva na kasar Switzerland, wanda zai samu wakilci daga kungiyoyin mabiya addinai daban-daban daga kasashen duniya. Bayanin ya ci gaba da cewa wakilan addinan musulunci da addinan kiristanci da yahudanci daga kasashe daban-daban za su samu halartar wannan taro, da nufin samara da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai. 469290