Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na muslim cewa; An yi kakkausar dangane da nuna wani fim din kyamar addinin musulunci a Amurka, wanda wani bayahuden kasar Canada da kuma yake da shedar zama dan kasa a Isra'ila ya shirya a jahar Penselvania. Bayanin ya ci gaba da cewa Musulmin kasar Amurka daga kowane bangare na kasar sun yi kakkausar suka dangane da hakan, inda suka bayyana hakan da cewa wani hankoro ne na haddasa kyamar addinin musulunci da musulmi a kasashen yammacin turai. 470274