Kamfanin dillanin dillancin Iqna ya nakalto daga daga kamfanin dillancin labaran SAN cewa; Shugaban bankin kasar Faransa ya bukaci da saka tsarin banki irin na Musulunci a cikin tsarin bankin kasar, saboda ingancinsa wajen daidaita lamurran harkokin tattalin arziki. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan wani shiri ne da Faransa ta bullo da shi da nufin jawo hankalin musulmi 'yan kasuwa daga kasashen musulmi daban-daban, wanda hakan zai karfafa tattalin arzikinta, musamman ta fuskar saka hannayen jari a bankunan gwamnati. 472051