Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na haberzinic cewa; Kungiyar yaki da dkar kayyade shekarun fara koyon kur'ani a kasar Turkiya ta fara karbar sa hannu daga al'ummar kasar domin tabbatar da cewa al'ummar kasar ba su amince da wannan dka ba. Bayanin ya ci gaba da cewa kungiyar ta dauki wannan mataki bayan da ta tabbatar da cewa mafi yawan al'ummar Turkiya ba su ammna da wannan ayar doka ba, a kan haka ta dauki nauyin fafutuka domin ganin an girmama ra'ayin jamar kasar. 472723