Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin intrnet Muslim cewa; Mahalarta taron addinai da aka gudanar a birnin Jeneva na kasar Switzerland sun kirayi dukkanin kafofin yada labarai da su taka rawa wajen kara kusanto da fahimta tsakanin mabiya addinai na duniya. Bayanin ya ci gaba da cewa wadanda suka halarci taron suna ganin cewa yin amfani da damar da kafofin yada labarai suke da ita daga dukkanin addinai za su iya taka rawa wajen kusanto da fahimtar mabiya addinai.472754