Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta Al'arab Anline ta watsa labarin cewa; Muhammad Mashmul mahardacin kur'ani na kasa da kasa ba'iraniye ne ya yi nasara a gasar Tajwidi da aka gudanar a kasar Libiya. Ita dai wannan gasa an kwashe mako guda ana tabkawa tsakanin mahalarta wannan gasa da suka fito daga kasashe daban-daban na larabawa da musulmi da ta hada hardar Kur'ani baki daya da kuma Tajwidi.
472674