Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar saudiyya cewa; Kwamitin zartarwa na gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa d akasa a Saudiyya ya gudanar da zamansa a birnin Makka mai alfarma. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasa ta samu halartar makaranta da kuma mahardata, wadanda aka girmama su bayan kammala gasar ta hanyar ba su kyaututtuka. 472906