Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na mufti cewa; Za a bude wasu ajujuwan koyar da ayyukan haji akasar Turkiya, da nufin ilmantar da masu zuwa gudanar da ayyukan haji da Umra a kasa mai tsarki. Bayanin ya ci gaba da cewa bude wadannan ajujuwa na da matukar muhimmanci ga dukkanin masu son zuwa kasa mai tsarki domin gudanar da ayyukan ibada na haji da umra, yanzu haka an fara gudanar da dukkanin shiryshirye na fara bayar da wannan horo. 473239