IQNA

Palastinawa Na Ci Gaba Da Tarewa A Cikin Harabar Masallacin Qods

15:19 - October 06, 2009
Lambar Labari: 1834391
Bangaren kasa da kasa; Palastinawa na ci gaba da tarewa a cikin harabar masallacin Qods mai alfarma, da nufin bayar da kariya ga masallacin wanda ke fuskantar barazanar rushewa daga yahudawan sahyuniya.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Kuwait cewa; Palastinawa na ci gaba da tarewa a cikin harabar masallacin Qods mai alfarma, da nufin bayar da kariya ga masallacin wanda ke fuskantar barazanar rushewa daga yahudawan sahyuniya. Bayanin ya ci gaba da cewa kimanin palastinawa 200 ne suke cikin harabar masallacin wadanda dukkaninsu shekarunsu sun haura 50, bayan da sojojin yahudawan sahyuniya suka hana duk wani dan kasa da shekaru 50 shiga cikin masallacin domin yin salla. 474401




captcha