An Fara Gudanar Da Taro Kan Karuwar Kyamar Muslunci A Turai
Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da wani zaman taro da ke yin dubi dangane da karuwar kyamar musulunci a kasashen yammacin turai musamman ma tun bayan kai harin sha daya ga watan satumba a Amurka.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa; An fara gudanar da wani zaman taro da ke yin dubi dangane da karuwar kyamar musulunci a kasashen yammacin turai musamman ma tun bayan kai harin sha daya ga watan satumba a Amurka. An fara gudanar da wannan zaman taro ne a bababn dakin taruka na ma'akatar harkokin wajen jamhuriyar muslunci ta Iran da ke birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran. 474845