Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da babban taro kan adana kayan tarihin Musulunci da kuma binin Qods gami da masallaci mai alfarma, wanda zai samu halartar manyan malamai daga sassa daban-daban na kasashen musulmi.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran kasar Jordan cewa; Za a gudanar da babban taro kan adana kayan tarihin Musulunci da kuma binin Qods gami da masallaci mai alfarma, wanda zai samu halartar manyan malamai daga sassa daban-daban na kasashen musulmi. Bayanin ya ci gaba da cewa taron zai mayar da hankali ne kan muhimman abubuwan da suka shafi tattara kayan tarihi da kuma muhimmancin da ke tatatre da adana su domin amfanuwar 'yan baya. 476558