IQNA

An Fara Gudanar Da Wani Taro Kan Fasahar Kur'ani A Birnin Madina

9:51 - October 15, 2009
Lambar Labari: 1837445
Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da wani zaman taro a birnin Madina mai alfarma dangane da fasahar kur'ani mai tsarki, wanda kuma masana daga sassa daban-daban na duniya na halartar zaman taron a matsayi na kasa da kasa.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga kamfanin dilalncin labaran kasar saudiyya cewa; An fara gudanar da wani zaman taro a birnin Madina mai alfarma dangane da fasahar kur'ani mai tsarki, wanda kuma masana daga sassa daban-daban na duniya na halartar zaman taron a matsayi na kasa da kasa. Daga cikin muhimman abubuwan da zaman taro zai mayar da hanakali kansu akwai batun yadda ya kamata a yi amfani da hanyoyi na hikima domin bayyana mu'ujizar kur'ani ta hanayar hikima ga sauran al'ummomi. 478227

captcha