IQNA

Kasar Kuwait Ta Kirayi Kasashen Musulmi Dangane Da Kara Fadada Dangantaka

17:10 - October 17, 2009
Lambar Labari: 1838186
Bangaren kasa da kasa; Jakadan kasar Kuwait a kasar Masar ya yi kira ga dukkanin kasashen muslmi dangane da kara karfafa dangantaka tsakanin kasashen musulmi, ta yadda hakan zai ba su damar cimma manufarsu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Masar cewa; Jakadan kasar Kuwait a kasar Masar ya yi kira ga dukkanin kasashen muslmi dangane da kara karfafa dangantaka tsakanin kasashen musulmi, ta yadda hakan zai ba su damar cimma manufarsu. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shi ne babban abin da musulmi suke bukata a halin yanzu wajen dawo da dukkanin karfinsu wuri guda. 479121

captcha