Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin internet na stocanalyst cewa; Za a gudanar da wani zaman taro na kasa da kasa dangane da harkokin bankunan Musulunci tare da baje kolin kayayyakin da suke da dangantaka da harkokin bankunan Musulunci a kasar Pakistan. Bayanin ya ci gaba da cewa taron zai samu halartar masana daga sassa daban-daban na kasashen musulmi, inda za su tattauna muhimman batutuwa da suke da danganataka wannan batu domin kara karfafa juna. 480669