Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa; a cikin wata zantawa da ta hada shi da fitaccen makarancin kur'anin na kasar Masar Sheikh Muhammad ahmad Bisyunini ya bayyana cewa; Jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei na girmama makaranta da mahardata kur'ani mai matuka daga ko'ina suka fito cikin fadin duniya. Ya ci gaba da cewa irin wannan girma da jagoran yake baiwa makaranta kur'ani na nuni da yadda fahimci girman kur'ani fiye da mutane da dama a duniya. 479693