Kamfanin dillancin labaran iqna a taron da ake gudanarwa na falsafar musluncia matsayi na kasa da kasa, ya gudanar da wata zantawa tare da wani daya daga cikin manyan malaman falsafar a jami'ar Japan cewa; Malaman falsafar Musulunci za su iya taka gagarumar rawa wajen warware da dama daga cikin amtsalolin da suka addabi al'ummomin duniya, musamman ma ta fuskokin tattalin arziki da siyasa. Ya ci gaba da cewz ya yi nazarin falsafar muslunci ya kuma fahimci cewa ita ce kawai za ta iya warware da dama daga cikin matsalolin al'ummomin duniya.491379