Amir PurPazeshk mai kula da ofishin yada al'adunb jamhuriyar Musulunci a kasar Spain a cikin wani bayani a hirar da ta hada shi da cibiyar yada harkokin kur'ani a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa; daya daga cikin hanyoyin da hukumar yada al'adu na Musulunci a Iran ke bi it ace tattaunawa ta addini a tsakanin kasashe. Ya kara da cewa; ta wannan hanya za mu iya yada al'adun Musulunci da ci gaban da muke son samarwa a tsakanin kasashen musulmi.
546260