Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna ta watsa rahoton cewa; ofishin da ke kula da yada al'adun Iran a ketare ya zama wakilin cibiyar nan mai kula da kara kusanci a tsakanin mazhabobi na Musulunci.
Ayatullahi Muhammad Ali Taskhiri babban sakataren kungiyar ta kara kusanci a tsakanin mazhabobi kuma mamba a komitin koli na hukumar al'adu a lokacin wata ziyara day a kai wa hukumar yada al'adun Iran ya bada labarin kulla yarjejeniyar aiki .
546848