IQNA

13:05 - March 11, 2010
Lambar Labari: 1896835

Ana Gudanar Da Bincike Kan Wajibcin Kare Muhalli A Musulunci Da Addanan Indiya

Bangaren al'adu da fasaha; an gudanar da bincike da nazari kan wajibcin kare muhalli da tsabtace shi a mahangar addinin Musulunci da kuma addinai a kasar Indiya.

Cibiyar da ke kula da harkokin addini a Iran a reshenta da ke hukumar da ke kula da yada al'adun Iran ta watsa rahoton cewa: an gudanar da bincike da nazari kan wajibcin kare muhalli da tsabtace shi a mahangar addinin Musulunci da kuma addinai a kasar Indiya. Kuma burin gudanar da wannan taro shi ne bayani kan addinin Musulunci a matsayinsa na addinin zaman lafiya da sulhu da kuma a dabra da haka a gudanar da irin wannan bincike a cikin addinin Musulunci da addinai a kasar Indiya. Kuma a gurin wannan taro an samu halartar wakilai masu yawa da kuma shugabannin jami'o'i.

550994
captcha