Daga Hadeddiyar daular larabawa ce cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta gwamnatin Hadeddiyar daular larabawa ta watsa rahoton fara gasar karatun kur'ani ta yan makaranta ta Sharja afadin kasar ta Hadeddiyar daular larabawa kuma a mako mai kamawa ne za a fara wannan gasa ta karatun kur'ani mai girma. Matakin farko na wannan gasa za a fara shi ne a ranekun sha uku da sha hudu na watan nan na Afrilu yayinda matakin karshe a gudanar da shi a ranekun sha takwas zuwa ashirin da biyu kuma wanda ya zo na daya zai samu kyautar dirham dubu goma na biyu dirham dubu bakwai yayin da matsayi na uku zai tashi da kyautar dirham dubu hudu.
558456