IQNA

A Karo Na Biyar Za A Gudanar Da Taron Inshorar Musulunci

19:16 - April 12, 2010
Lambar Labari: 1906172
Bangaren kasa da kasa; Za agudanar da wani zaman taro na kasa da kasa na inshorar musulunci a birnin Dubai kasar hadaddiyar daular larabawa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani rahoto da ya nakalto daga shafin yanar gizo na ameinfo an bayyana cewa, za agudanar da wani zaman taro na kasa da kasa na inshorar musulunci a birnin Dubai kasar hadaddiyar daular larabawa. Bayanin ya ci gaba da cewa taron zai samu halartar masana kan harkokin tattalin arziki daga kasashe daban-daban na duniya, wadanda za su gabatar da laccoci dangane da muhimmanci inshore, da kuma yadda musulunci ya tsara aiwatar da ita.560591



captcha