IQNA

An Shirya Gasa Kan Haumiya Mafi Kyau A Kasashen Musulmi

19:47 - April 14, 2010
Lambar Labari: 1907385
Bangaren kasa da kasa; An shirya gudanar da wata gasa kan hasumiya mafi kyau a kasashen msulmi, wadda kungiyar raya al'adu da ilimin addinin musulunci ta kasa da kasa ta shirya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga bangaren hulda da jama'a na kungiyar ISESCO an habarta cewa, An shirya gudanar da wata gasa kan hasumiya mafi kyau a kasashen msulmi, wadda kungiyar raya al'adu da ilimin addinin musulunci ta kasa da kasa ta shirya. Bayanin ya ci gaba da cewa, yanzu haka dai an gabatar da hotuna na masallatai da daman a kasashen musulmi da ma wasu wadanda ba a cikin kasashen musulmi a gina su ga kungiyar, domin tantance hotunan masallatan da za a yi amfani da su a cikin gasar. 561813

captcha