Muhammad Alishavandi shugaban da ke kula da bangaren al'adu a ma'aiakatar harkokin addini a wata tattaunawa da cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna daga yankin Yazd ta watsa rahoton cewa; ma'aikatar da ke kula da harkokin addini ta jibanci nauyin rubuta Kur'ani da marubta na fadin kasar Iran za su rubuta a Yazd. Har ila yau ya kara da cewa; rubuta kur'ani mai girma za a kammala shi a ranar sha tara ga watan Tir na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira kamariya a daidai lokacin zagayowar ranar mab'ats na ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka. Kuma an gayyato shahararrun marubuta ne kimanin arba'in da biya zuwa yankin na Yazd.
564490