Bangaren kasa da kasa: a ranar biyar ga watan Ordebehesht na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara a jami'ar Alhayat da nazarin Musulunci ta jami'ar Sharja a kasar Hadeddiyar daular aka fara taro kan tafsirin kur'ani mai girma kan ayoyin da suka yi magana da bayani kan abu guda.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta gwamnatin hadediyar daular larabawa ta watsa rahoton cewa: a ranar biyar ga watan Ordebehesht na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara a jami'ar Alhayat da nazarin Musulunci ta jami'ar Sharja a kasar Hadeddiyar daular aka fara taro kan tafsirin kur'ani mai girma kan ayoyin da suka yi magana da bayani kan abu guda. A wajen wannan taro an samu halartar kimanin masu fassarar kur'ani hamsin dam asana da masu nazari da bincike daga kasashen musulmi da larabawa da kuma wasu mabiya addini da wakilan gwamnatin Hadeddiyar daular larabawa.
568725