Bangaren kasa da kasa: hukumar laraba mai lura da hakkin dan adam ta yi Allah wadai da nuna adawarta a fili kan yadda ake nunawa yan shi'a a wannan kasa wariya da azabtar da su a kasar Saudiya.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ikna bayan ta nakalto daga gidan talbinin na Rasid ta watsa rahoton cewa hukumar laraba mai lura da hakkin dan adam ta yi Allah wadai da nuna adawarta a fili kan yadda ake nunawa yan shi'a a wannan kasa wariya da azabtar da su a kasar Saudiya.Ita dai wannan hukumar kare hakkin dan adam a tsakanin kasashen larabawa da ked a cibiyarta a birnin Alkahira na kasar Masar kamawa da yin awangaba da Hasan Ali Almaki fitaccen dan Shi'a da fakewa da zargin yana gudanar da sallar juma'a a gidansa a garin alkhubar ya sabawa hakkin dan adam da mahukumtan Saudiya suka yi.
568850